Lauyan Dalibin nan dake jami’ar taraiyya ta garin Dutse a jihar Jigawa, mai suna Aminu Adamu, wanda aka kama bayan ya yi wani rubutu akan mai dakin shugaban kasa, Aisha Buhari, a shafinsa na twitter, Ya ce ya nemi a bada belin dalibin domin ya samu damar fara rubuta jarabawarsa ta karshe a jami’ar a ranar 5 ga watan da muka shiga na Disamba.
An kama Aminu Adamu ne bayan ya rubuta cewar, Mama ta ci tayi kiba da kudin Talakawa, wanda ya wallafa rubutun a shafinsa na Twitter.
Lauyansa mai suna CK Agu, ya fadawa manema Labarai cewa an gurfanar da wanda yake karewar ne a Abuja, kuma bai amsa cewar ya aikata lefin da ake tuhumarsa dashi ba, ya kara da cewa tun a ranar 25 ga watan Nuwamba ne ya nemi a bada belin dalibin amma aka hana.
A cewarsa Kotu ta umarci jami’an yansanda dasu gabatar ta takardar neman bada dalibin beli wanda kuma shine zai sa kotun ta yi duba kan bukatar tasu a yau ko gobe, kuma tuni aka yi hakan.