Wata dalibar makarantar sakandiren ’yan mata da ke birnin Nnewi a Jihar Anambra mai suna Ejikeme Mesoma da ake zargi da yin karawa kanta maki a sakamakon jarabawar UTME, ta magantu.
Ejikeme ta yi ikirarin cewa ba ta da ikon yin sakamakon boge a shafin hukumar JAMB , inda ta kara da cewa ta kasance yarinya mai hazaka, inda take samun matsayi na farko tun daga makarantar firamare.
A wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafinta na Facebook, ta bayyana cewa an gayyace ta zuwa ofishin jami’an hukumar tsaron farin kaya DSS inda aka kai bayaninta, kuma an shaida mata cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kafin JAMB tayi magana a kafafen yada labarai…
Idan za’a iya tunawa JAMB, a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, ta ce dalibar ta tafka magudi a sakamakon farko, inda ta yi barazanar janye sakamakon da kuma gurfanar da ita a gaban kuliya.