Biyo bayan barazanar da ‘yan bindiga suka yi na kai hari Makarantar Koyon aikin shari’a ta kasa dake Kwali a birnin taraiyya Abuja, A yanzu haka Ma’aikatar Ilimi ta kasar bayar da umarnin rufe dukkan makarantun da ke Abuja babban birnin taraiyyar Najeriya.
Umurnin ya zo ne a daidai lokacin da dalibai ke rubuta jarabawar zango na uku, kuma a wani mataki na cika umarnin da ma’aikatar ilimi ta bayar, Hakan tasa Hukumomin makarantun suka yi gaggawar kammala rubuta jarabawar da tayi saura ga daliban.
Wani dalibin karamar Sakandire ta Kubwa da ke Abuja, ya koka kan yadda malamansu suka sa su rubuta jarabawar darussa 13 a ranar Talata.
Dalibin ya ce wasu daga cikinsu sun razana, saboda fargabar yiwuwar kai masu harin ta’addanci. Mazauna Abuja sun shiga cikin fargaba sakamakon karuwar masu satar mutane da kuma harin kwanton bauna da aka yiwa wasu sojoji a karshen makon jiya.