A yaune Kungiyar Dalibai ta kasa zata gudanar da zanga-zanga domin nuna adawarta da karin kudin makaranta da aka yi a manyan makarantun kasar nan.
Kungiyar ta kudiri cewar ‘ya’yanta zasu yi zanga-zangar a jami’ar Legas, tare da gargadin jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS da kada su hana daliban ‘yancinsu na yin zanga-zangar.
Kakakin kungiyar Giwa Temitope ne ya baiyana haka lokacin da yake mayar da martani kan sanarwar da hukumar DSS ta fitar, Wanda ta baiyana cewar wasu ‘yan siyasa sun dauki nauyin dalibai domin yin zanga-zanga akan gwamnatin taraiyya dangane da halin da kasa ke ciki.
Sai dai ya fadawa manema Labarai cewar zanga-zangar su ta neman yanci ne a kokarinsu na ganin an janye karin kudin makaranta da aka yiwa daliban.