Hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA), ta bayyana cewa akwai yiwuwar zata dage fara gasar cin kofin kwallon ta duniya ta shekarar 2022.
Tun da fari dai, hukumar ta tabbatar da ranar 21 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za’a fara gasar ta bana, inda kasar Senegal zata barje gumi da Netherlands a wasan farko, a daidai lokacin da mai masaukin baki Qatar zata buga wasan ta farko da kasar Ecuador a ranar.
Sai dai rahotanni sun bayyana cewa hukumar ta dage wasan mai masaukin bakin zuwa ranar Lahadi, 20 ga watan na Nuwamba.