Da yuyuwar a sake fuskantar tafiya yajin aikin jami’oi a kasar nan a shekara mai zuwa, sakamakon kason da aka ware masu cikin kunshin kasafin kudin shekara mai zuwa bai taka kara ya karya ba, kamar yadda kungiyar malaman jami’oi ta kasa ta baiyana.
A hirarsa da manema labarai a jiya, Shugaban kungiyar na kasa, farfesa Emmanuel Oshodoke, Ya ce a yayin yakin neman zaben shugaban kasa Bola Tinubu, ya yi alkawarin karawa kasafin fannin ilimi kimanin kaso 15 cikin 100.
Sai dai kuma y ace kungiyar ta baiyana mamakinta kan yadda aka warewa bangaren ilimi naira tiriliyan 2 da bilyan 18, wanda ya kama kaso 7 da digo 9 cikin 100 na kasafin kudin, kuma hakan ya saba ta tanadin hukumar bunkasa ilimi da raya al’adu ta majalisar dinkin duniya UNESCO, wadda ta bukaci a rika warewa bangaren kaso 26 cikin 100.
Dagan an shugaban kungiyar malaman jami’oin ta kasa ya shawarci gwamnati da ta yi zama na musamman da ‘yan majalisar zartawa domin karawa fannin ilimi kaso mai tsoka a cikin kasafin kudi.