Mai rikom mukamin shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Abba Kawu Ali, ya bayyana damuwa akan gazawar kotun daukaka kara na sakin takardun hukuncin shari'ar zaben gwamnan Kano ga tawagar lauyoyin Jam'iyyar.
Ali, a cikin wata sanarwa, ya ce batutuwan kwanaki da lokaci suna da matukar muhimmanci wajen shirye-shiryen daukar matakin daukaka kara a irin wannan yanayi.
Ya nunar da cewa mai kara yana da damar kwanaki 14 kawai don kammala shirinsa, kuma asarar kwanaki 4 daga cikin wadannan kwanaki 14 kamar kafa tarko ne ga mai kara.
Ya kuma yi zargin cewa da gangan ake kokarin kawo cikas ga jam’iyyar NNPP.
Ya nanata kudurin jam’iyyar na yin aiki a cikin tsarin doka don dawo da hakkokinta a kotun koli.