On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

CIRE TALLAFI: Gwamnatin Jihar Kano Na Shirin Fara Sayarwa Al'ummarta Kayan Abinci A Farashi Mai Rahusa

Idan kana cikin masu jiran tallafin gwamnatin jihar Kano bayan cire tallafin man fetur, to a iya cewa  jira ya kare yayin da gwamnatin  ta fitar da tsare-tsaren agajin rage radadi.

Sai dai ga dukkan alamu tallafin yazo cikin sabon yanayi domin gwamnatin jihar na shirin siyan hatsi daga gwamnatin tarayya da kuma sayarwa a  farashi mai rahusa ga mazauna jihar ta Kano.

Gwamnan jihar, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka a lokacin wani taron tattaunawa na farko da mambobin kwamitin kyautata ‘Da’a a cikin  al’umma CRC daga kananan hukumomi 44 a jiya.

A bangaren sufuri kuwa, Gwamnan ya ce ana shirin farfado da motocin Kanawa domin taimakawa dalibai da mata da sauran nau’o’in mabukata kyauta.