Wata tsohuwar Akori Kura da ake 'daukar itace da ita, ta koma motar daukar marassala lafiya wuta ta juya motar daukar marasa lafiya domin ceto mata masu rayukan mata masu juna biyu, Sannan Kuma an sayi wani kwandon zuba shara a kan Naira Dubu 100. “A wasu asibitocin, shugabanninsu nada ikon cire kiman Naira miliyan biyu, yayin da ka’idar ta ce ba za su iya fitar da fiye da naira dubu Hamsin ba, wasu kuwa na ikirarin cewa sun yiwa wadansu dakunan asibitocin fenti, Amma magana ta gaskiya ba'a yi wannan fentin a hukumance ba.
Mai Rahoto Kolawole Omoniyi.
TSOHUWAR MOTAR DAUKAR ITACE WADA TA KOMA MOTAR DAUKAR MARASSA LAFIYA
wannan Tsohuwar motar daukar kayan mai launin rawaya, an Samar da ita ne domin jigilar kaya masu nauyi , musamman itacen yin girki daga wani kauyen zuwa wani a kewayen garin Jeli dake karamar hukumar Tudunwada ta nan jihar Kano.
To sai dai wani hanzari ba gudu ba, Da zarar Dare ya kawo jiki, tsohuwar motar guda daya da ake amfani da ita a garin mai tazarar kilomita 120 daga birnin Kano a kodayaushe a shirye take domin ceto duk wani mara lafiya saboda rashin ingantaccen Asibiti da rashin kyawun hanyar da zata kaika kauyen.
Duk da kasancewar motar ba ta da cikakkiyar lafiya da kuma rashin kyawun Yanayi ga marassaa lafiya, mai motar, Haruna Sani, Dan shekaru 45 a duniya, ya ce ya yi amfani da motar wajen ceto rayukan mutane sama da 80 , Wanda akasarinsu mata masu juna biyu ne, a garin a shekaru 15 da suka gabata.
Tsohuwar motar ta zamarwa mutanen yankin motar daukar marassa lafiya a duk lokacin da wani Abu na Neman agajin gaggawa ya taso, duk da kasancewar ta siradi tsakanin mutuwa da rayuwa.
WATA MATA MAI CIKI WADDA TAYI RASHIN SA'A TA MUTU A CIKIN MOTAR BAYAN WATA DOGUWAR NAKUDA DATA FUSKANTA.
Wata Mata Mai Ciki wadda tayi rashin sa'a ta mutu a cikin motar bayan wata doguwar Nakuda data fuskanta.Duk da cewar malam Sani yana kokarin tallafawa jama’a ne, To sai dai Hassana Ibrahim ba ta yi sa’ar samun haka ba, Duk da cewar an kwantar da ita cikin tsohuwar motar domin kaita Asibiti, To sai dai kuma motar ta samu matsala ta bangaren makunninta.
Duk da cewar an hada tawagar wasu manyan mutane domin tura motar har tsawon mintuna 30. Daga nan aka fara tafiyar sama da kilomita 20 zuwa asibiti mafi kusa. Sai dai kash Hassana ta rasu a hanya ba da jimawa ba.
Bayan haka ne , Motar ta fara yin tafiya wadda za’a shafe tsawon sama da Kilomita 20 kafin a kaiga zuwa Asibitin, Sai dai kuma abun alhinin Hassana ta riga mu gidan gaskiya akan hanyar kaita asibitin.
‘’ Watakila da Hassana ba zata mutu ba, Da ace motar tawa tana da cikakkiyar koshin lafiya’’ A cewar Sani.
‘’Tana fama da nakuda a cikin motar da aka kwantar da ita, wadda muka fara turawa tsawon mintina 30, har ta kaiga karfinta ya ‘kare, yayin daga bisani kuma ta ce ga garinku nan, a lokacin da muke gab da ‘karasawa Asibitin.
MALAM SANI DIREBEN MOTAR
Asibitin Sha Ka Tafi na garin Jeli, Na da tazarar kilomita 100 daga gidansu marigayi ya Hassana, Sai dai kuma bashi da isassun kayan kiwon lafiya da ake bukata domin sakara mai juna biyu. Wannan shine dalilin da yasa aka dauki Hassana zuwa wani asibitin mai tazarar kilomita 20 kafin ta gamu da ajalinta.
ASIBITIN GARIN JELI
TAKADDAMA AKAN WANDA YA KAMATA YACI GAJIYAR SHIRIN BHCPF , YA KAWO KATSALANDAN WAJEN AIWATAR DA SHIRIN A ASIBITIN JELI
Asibitin Jeli na cigaba da kasancewa a yanayi na ban takaici duk kuwa da kasancewar daya daga cikin masu cin gajiyar hirin Asusun Kula Da Lafiya Kyauta Na Gwamnatin Taraiyya [BHCPF]. Shekaru biyu bayan Kano a matsayin na jiha ta fara aiwatar da shirin, Sai dai kuma babu wani tasiri da shirin ya haifar ga Asibitin.
Ga dalilin da suka haddasa samun hakan, Daga cikin masu ruwa da tsaki na Asibiyin Jeli da Yaryasa dake a mazabar Yaryasa ta karamar hukumar Tudunwada, ana ta takaddama kan wanda ya da ikon cin gajiyar shirin na BHCPF.
Wani Ma’aikacin Hukumar kula da shirin Temake-keniyar Lafiya na jihar Kano, Akarami Nuhu Aliyu, (KSCHMA) dake Asibitin Yaryasa , ya yi ikirarin cewa yana cikin wadanda aka horas domin gudanar da shirin a Asibitin Yaryasa kafin a karkatar dashi daga Asibitin.
A cewarsa, an karkatar da shirin ne saboda rashin warware takaddamar da ke tsakanin tsohon shugaban Asibiyin Yaryasa, Magaji Ubale, da kuma tsohon shugaban shugaban sashensa, Suraju Sabayuki.Dukkanin mutanen da zasu ci gajiyar shirin yan asalin garin Yaryasa ne, Amma saboda karkatar dashi da aka yi, Jami’an Asibiyin Jeli ne kadai ke da ikon yin ta’ummuli da kudin gudanar da shirin dake cikin Banki.
" Garin Jeli yana da nisan sama da kilomita 20 daga Garin Yaryasa, Sai dai wadanda suke a cikin shirin ba za su iya biyan kudin abun abun hawa daga kauyen garin nasu ba, wanda ya kama naira 800, sai kuma tarnakin aiwatar da shirin a dukkanin asibitocin biyu’’ kamar yadda Aliyu ya baiyana.
Kazalikaza Wani dattijo mai bukata ta musamman dan shekaru 65 a duniya, Shehu Garba, da kuma Babban Limamin garin Yaryasa Iliya Saleh Dan shekaru 80 a duniya, na daga cikin wadanda suka yi rajistar cin gajiyar shirin . Sun koka da cewa duk wani fatansu na samun kula da lafiya kyauta a Asibitin Garin Yaryasa ya gamu tazgaro sakamakon an karkatar da shirin.
Malam Shehu Garba Da Iliya Saleh
Koda aka tuntube su ta wayar tarho, Ubale da Sabayuki sun musanta cewa suna da wani takun sa’ka a tsakaninsu. Ubala ya danganta rashin aiwatar da shirin bisa zargin karkatar dashi da tsohon shugabansa yayi, Sai dai kuma Sabayuki ya jaddada cewa matakin da aka dauka ya samu amincewar dukkanin masu ruwa da tsaki.
Kokarin da wakilinmu ya yi na samun karin haske kan wannan zargi, Hakan ta sa shi kai ziyarar ba zata zuwa garin na Jeli, wanda ake shan wahala kafin a isa garin wanda mutuwar marigayiya Hassana ta faru.
Hanyar zuwa garin Jeli a Lalace take, Yin Tuki a kanta abune mai wahalar gske. Aikin gina gadar dake kan hanyar garin ya kara dagula lalacewar ta.
A lokacin da wakilinmu ya isa wani bangare na hanyar, Dole tasa ya ajiye motarsa a gefen hanya, Sannan ya hau ‘Dan Acaba domin cigaba da tafiya.
LALACEWAR DA HANAYR GARIN JELI TA YI
Daga karshe dai ya samu nasarar ganawa Sale Haruna, wanda ya kasance shugaban Asibitin Jali, Wanda kuma shine kadai cikakken ma’aikaci a Asibitin.
Tun a watan Maris na shekarar 2020 da aka nemi da ya karbe ikon tafiyar da shirin, Saia i kuma Haruna bai iya ba da jerin sunayen wadanda suka yi rajista a karkashin shirin a Asibitin na Jeli ba lokacin da wakilinmu ya ziyarce shi a ranar 7 ga watan Yulin 2022.
‘’Hukumar Kula da Kananan Asibitoci ta jihar Kano ta ce Asibitin Jeli ne aka tantance domin cin gajiyar tsarin, wanda kuma suka sani, na samu kira ne kawai daga shugabanmu na wancan lokacin (Sabayuki) a tsakanin cikin watan Maris na 2020, kan cewar a hali yanzu za’a rika aiwatar da shirin na BHCPF a Asibitin na Jeli PHC.
‘’ Darakta daga KASHMA,[ Dr Abdullahi ] A watan yunin 2022 ya kirani kan cewar tawagar jami’ansu zasu zo domin warware matsalar bada jimawa ba’’ kamar yada ya baiyana.
BAYANIN ASUSUN BANKI KAN GUDANAR DA SHIRIN BHCF A ASIBITIN JELI
Watanni bayan alkawarin da hukumar KASHMAS ta yiwa Haruna domin sabunta bayaann wadanda zasu ci gajiyar shirin a Asibitin na Jeli, Wakilin namu ya tuntubi shugaban ta wayar tarho a ranar 9 ga watan Augustan 2022. Amma yace babu wani da ya ji daga hukumar.
BUGU DA ‘KARI, WATA MATA MAI SHAYARWA TA RASU AKAN BABUR A GARIN NA JELI
Haruna ya tabbatar da rasuwar wata mata mai shayarwa mai suna Amina Salihu. Shugaban Asibitin ya ce ya tura Amina dake fama da karancin jini -zuwa wani asibiti mai inganci da ke Tudunwada, amma ta mutu a kan babur a kan hanyarta ta zuwa asibitin.
Da aka tuntubi Daraktan kula da shirin a Huumar ta KASCHIMA, Dt. Abdullahi Sahad Ahmed, ya bayyana cewa, an mayar da shirin ne zuwa Asibitin Jeli ne kasancewar Asibitin Yaryasa yana da makamancin wannan tsari a cikinsa ga ma’aikatan gwamnati da kuma wani na marasa galihu, yayin da Asibitin Jeli babu mutum da yake amfana da irin wannan tsari.
AN BAR JIHAR KANO A BAYA, SHEKARU UKKU BAYAN KARBAR KASONTA NA SHIRIN ASUSUN KULA DA LAFIYA KYAUTA NA GWAMNATIN TARAIYYA ( BHCPF)
An fara aiwatar da cikakken shirin ne a shekarar 2019, wanda a matakin farko gwamnatin taraiyya ta raba naira bilyan 6 da milyan 500 ga jihohi 15, inda jihar Kano ta samu naira milyan 948.
Duk da wannan makudan kudi da kuma kaso na biyu da aka saki a shekarar 2022, Shirin bai haifar da wani Da mai ido ba, a mafi akasarin asibitoci 881 dake cin gajiyar shirina ziyar gani da ido da aka kai wuraren.
Masu ruwa da tsaki sun danganta matsalar da ake samu da Cin Hanci da Almubazzaranci da kuma nuna Sakaci wajen gudanar da aiki da sauransu.
MUTUWA, DA CAKUDA SUNAYEN WADANDA ZASU AMFANA DA SHIRIN YA KAWO TAZGARO WAJEN AIWATAR DA SHIRIN NA BHCPF A ASIBITOCI DA DAMA.
Ga misali, a asibitin Tsohon-Gari da ke karamar hukumar Tudunwada, an hana Mutan i 298 da ke Mazabar Tsohon-Gari cin gajiyar shirin na BHCPF a cikin shekaru biyu da suka wuce bayan rasuwar shugaba na Biyu mai kula da gudanar da shirin, wanda aka fi sani da 2-IC mai suna , Sani Salisu.
Umar Abdu, wanda ya kasance Shugaban Asibitin, ya ce Salisu, wanda yana daya daga cikin wadanda suka sanya hannu kan asusun shirin kiwon lafiya kyauta na gwamnatin taraiyya BHCPF, ya rasu a ranar 14 ga watan Octoban 2020. Ya yi ikirarin cewa ya rubuta wa Hukumar kula da Asibitoci ta jihar kano KPHCMB wasika tun a cikin Satumbar 2021 tare da e takardar dake tabbatar da mutuwar marigayi Salis, domin a maye sunansa da wani, Amma shuru ka ke ji babu wani labara.
Matsalar da ke faruwa a Asibitin Tsohon-Gari ta yi daidai da wadda Asibtin Middle Road dake karamar hukumar Fagge ke fuskanta, inda shugaban kwamitin cigaban unguwar Alh. Yau Muhammed ya rasu watanni shida da suka gabata, wanda hakan yayi sanadin yin cikas a bangaren gudanar da shirin.
Hauwa Umar Fagge wadda ta kasance shugabar Asibitin, ta ce daga baya ta yi nasarar maye gurbin sunan Muhammed da sabon shugaban kwamitin mazabar Anthony Monday - watanni biyu da suka gabata. Sai dai kuma, duk da haka, ba’a fara gudanar da cikakken shirin na BHCPF sakamakon rashin samun izinni daga Hukumar KPHCMB da kuma tarin kura-kuran dake cikin rijistar masu cin gajiyar shirin.
“Babu lambar waya a kashin farko na sunayen da suka ba mu. Sannan kuma abu ne mai wahalar gaske sake bibiyar wadanda suka yi rijista da shirin. Sun canza mana jerin sunayen ne a makon farko na watan Yulin 2022 lokacin da muka gano cewa mutane 27 ne kawai cikin 68 da ke cikin jerin sunayen suka kasance yan asalin wannan Unguwa, sauran 41 kuma sun fito ne Sabongari Gabas ne” A cewar ta.
Kazalika Asibitin Abasawa da ke Mazabar Tsamiya Babba a karamar hukumar Gezawa yana da masu rajistar cin gajiyar shirin biyu ne kacal. Shugaban Asibitin Kabiru Yahaya, ya ce ba’a taba samun mutanen ba a lokacin da aka neme su.
“Muna da wadataccen Magani sai dai kawai sun bamu sunayen mutane biyu da ba’a san inda suke ba’’ A cewarsa.
SUNAYEN MASU CIN GAJIYAR SHIRIN A ASIBITIN ABASAWA
Hakazalika, akasarin wadanda suka yi rajista a karkashin shirin a Asibitin Jaba sun fito ne daga karamar hukumar Minjibir, mai tazarar kilomita 60 daga nan Kano, kamar yadda wasu masu amfana da shirin daga Gandun Albasa da ke cikin birnin Kano suka shiga jerin sunayen wadanda zasu amfana da shirin a Asibitin Yaryasa dake a karamar hukumar Tudunwada.
Jihar Kano ta samu masu cin gajiyar shirin dubu 79 a kashin farko na shirin asusun kula kiwon lafiya kyauta na gwamnatin taraiyya a nan kano BHCPF. Sai dai kuma wakilinmu ya fahimci cewa anyi amfani da Alfarma wajen shigar da sunayen
Misali, shida daga cikin Asibitoci 381 masu amfana da shirin sun sami mutum daya kadai ne daga wajensu, sannan kuma Asibitoci 29 suna da kasa da mutane 10 kowannensu a jerin sunayen, kamar yadda bayanan da Hukumar KSCHMA ta fitar suka nuna.
HUKUMAR KASCHMA TA ZARGI MASU UNGUWANNI DA SHUGABANNIN KWAMITIN UNGUWANNI DA YIN COGE A CIKIN TSARIN.
Da take mayar da martani, Hukumar KASCHMA, Wadda ita ce keda alhakin aiwatar da shirin Insorar Lafiya na kasa NHIS da kuma shirin na BHCPF, ta danganta matsalolin da aka samu a cikin shirin, da yin rijista har sau biyu , sakamakon dogaro da shugabannin al’umma, wadanda suka yi zargin sun yiwa shirin ungulu da kan zabo.
Da yake jawabi a madadin Babbar Sakatariyar Hukumar, Halima Muhammad Mijinyawa, Daraktan kula da shirin Dr. Abdullahi Sahad Ahmed Ya ce an sake fitar sunayen wadanda zasu ci gajiyar shirin sannan kuma aka karkatar da sunayen.
“Mun dauka cewar Masu Unguwanni da Shugabannin Kwamitin Unguwannci sun san mutanensu sosai, A saboda haka muka ba su damar tantace sunayen amma yawancinsu sun sanya sunayen mutanen da suka sani ne kawai ba tare da la’akari da wurin da suke ba, Misali, mun gano cewa daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin Jami’in tsaro ne na Civil Defence wanda bai cancanta ace yana cikin shirin ba,” a cewarsa.
Dr. Ahmed ya ce a yanzu haka hukumar na gudanar da tantancewa a wuraren domin tabbatar da cewa duk wanda zai gajiyar shirin ya mika lambar shaidarsa ta zama dan kasa (NIN) kafin su ci gaba da cin gajiyar shirin.
FITAR DA CAKIN NAIRA DUBU 100 A HUKUMANCE DOMIN SIYEN KWANDON SHARA YASA AN BADA CIN HANCIN DUBU 65.
An kuma gano wata cuwa-cuwa da aka yi a Asibitin Jaba inda shugabar Asibitin Samira Ibrahim Ayuba, ta fitar da cakin kudi guda bakwai domin cire kudi daga asusun BHCPF a cikin kwana daya. A
Ta ce cakin kudade - wanda aka fitar a ranar karshe ta shekarar 2021 - an yi haka ne domin siyan wasu kayan aiki da magunguna da biyan kudin ma'aikata na wucin gadi.
Samira ta ce an fada mata cewar dole ne duk wasu kudaden da ba a yi amfani dasu ba dake cikin asusun bayan watan Disambar 2021, A saboda haka aka yi gaggawar cire kudin a cikin sa'o'i 11. Amma bayan ta fahimci cewar akwai matsaloli, ta umurci dukkanin wadanda suka amfana da shirin su dawo a kudaden.
Daya daga cikin wadanda ake zargin ta cire kudi, ta bayar da cakin Naira 100 domin siyan kwandon shara guda daya. Daga baya ta je kasuwa, ta sayi kwandon sharar a kan Naira dubu 35-000, sannan ta nemi a ba ta Naira dubu 65 daga hannun mai siyarwar, Kabiru Ibrahim.
kwandon shara da Samira ta sayo
“Na je kasuwar Sabongari na sayi kwandon shara, sai na ce wa mai siyarwar (Ibrahim) ya karbi kudinsa dubu 35 ya ba ni ragowar kudin Dubu 650 a tsabarsu ,” kamar yadda ta baiyana.
“Daga baya aka ce min yin hakan ba daidai ba ne. Na koma wurinsa, na ba shi Lambar asusun BHCPF domin ya taimaka ya saka naira dubu 70, Bayan haka, na biya shi sauran kudinsa naira Dubu 5 daga Albashi nan a naira Dubu 50 da nake karba.
LITTAFIN CAKIN KUDI NA BANKI YA KAWO TSAIKO WAJEN AIWATAR DA SHIRIN ASUSUN KIWON LAFIYA KYAUTA NA GWAMNATIN TARAIYYA BHCPF A KANAN HUKUMOMI 6 NA JIHAR KANO.
Dukkanin Asibitoci 51 da ke a karkashin shirin na BHCPF a cikin kananan hukumomin shida na jihar kano, da suka hada da Tsanyawa, Bichi, Kunchi, Garko, Makoda da Dambatta har yanzu ba su fara aiwatar da shirin ba bayan shekaru biyu da soma shi.
Wasu daga cikin jami’an da abin ya shafa a karamar hukumar Tsanyawa sun fadawa wakilinmu cewa, duk da cewa sun shafe sama da shekara guda suna ganin sakon banki daga Hukumar KPHCMB da KASHMA, amma ba za su iya fitar da kudaden ba saboda rashin littafin cakin kudi daga bankunansu.
Asibitin Tsanyawa mai dauke da rajistar mutane 583 dake a karkashin shirin, Ko mutum daya babu wanda ya amfana da shirin.
"Muna da sama da Naira 4-609-520 a asusun mu, sai dai kawai suna saka mana kudaden ne amma ba za mu iya cirewa ba saboda rashin cakin kudi da zamu yi amfani dashi, in ji shugaban Asibitin, Sharhabil Habeeb.
"Yawancin Mutanen dake karkashin shirin suna zuwa neman magani amma ba za mu iya yin komai ba, koyaushe muna rokonsu da su yi hakuri," A cewarsa.
Da aka tuntubi Babban Sakataren Hukumar Kula Da Asibitoci ta jihar Kano KPHCMB Dr. Tijjani Hussain, ya ce ba a fara aiwatar da shirin a kananan hukumomin shida ba saboda jinkirin bayar da litattafin Cakin Kudi , amma kuma yaki fadar sunayen bankunan.
Dr. Hussain ya ce bayan bin diddigin da aka yi na tsawon shekaru biyu, hukumar ta bukaci bankin ya mayar da dukkan kudaden shirin na BHCPF da ke hannun ta, tare da gaggauta bude wani asusu a wani banki domin gudanar da shirin.
TAKUNKUMIN HUKUMAR KPHCMB YA KAWO TSAIKO WAJEN SAMUN WANI ABU DAGA HUKUMAR BUNKASA KIWON LAFIYA A MATAKIN FARKO TA KASA A MAFI YAWA DAGA CIKIN ASIBITOCIN JIHAR KANO
Duk da cewa kudaden tafiyar da shrin ana tura su ne kai tsaye ga Asibitoci 381 dake amfana da shirin sai dai takunkumin da aka saka daga bangaren hukumar Bunkasa lafiya a matakin farko ta kasa wanda ya shafi kudaden tafiyar da ayyuka da gyaran kayan aiki da biyan ungozoma da daukar sabbin ma’aikata ya sa an dakatar da shirin sama da shekara guda a wasu asibitocin a nan Kano.
An dakatar da gine-gine da gyare-gyaren da ake yi a Asibitin Gungara da na Kademi da Garmarya da ke karamar hukumar Gaya, bayan da aka yi zargin cewa an saka masu takunkumi.
AIKIN DA YA TSAYA CAK A ASIBITIN GUNGAYA
AIKIN ASIBITIN GARMAYA
AIKIN ASIBITIN GARMAYA
HUKUMAR KPHCMB TA KARE MATAKIN SAKA TAKUNKUMI, INDA TA YI ZARGIN YIN RUFA-RUFA WAJEN AIWATAR DA SHIRIN
Ma’aikatan dake da ruwa da tsaki wajen aiwatar da shirin a matakin jiha sun musanta zargin cewa sun saka takunkumi wajen aiwatar da shirin domin wata bukata ta kashin kai.
Da yake mayar da martani akan tambayar da wakilinmu ya yi masa, Dr. Tijjani Hussain, Babban Sakataren Hukumar KPHCMB, ya ce matakin ya shafi ma’aikatan wasu asibitoci ne kawai saboda rashin yin komi a faiyace. “A wasu Asibitocin , wani shugaban asibiti zai ciro kusan Naira miliyan biyu yayin da ka’idar ta ce ba za su iya fitar da sama da Naira Dubu 50 ba; wasu za su ce sun yiwa wasu dakunan asibiti fenti kuma ba a yi hakan ba.
Ya kara da cewa takunkumin ya kuma shafi biyan ma’aikatan ungozoma da ma’aikatan wucin gadi dama daukar sabbin ma’aikata saboda yadda ake tafka kura-kurai a harkar daukar ma’aikata da biyan albashi. Ya kuma ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a shawo kan dukkan kalubalen da aka gano.
Duk da haka, malam Sani – direban dake tallafawa jama’a a garin Jeli , ya baiyana cewa motarsa mai shekaru 15 ba za ta iya cigaba da kasancewa a yadda take ba din-din din.
Sai dai ya yi fatan cewar mutuwar Hassana zata kasance ta karshe da za a iya samu daga bangare mata masu dauke da juna biyu dake mutuwa ba zato ba tsammani a garin , idan har gwamnatin jiha ta samar da ingantaccen Asibiti da isassun ma’aikata ga mazauna kauyen.
Wannan rahoton nA Hadin gwiwa ne da Cibiyar bin didddigi kan Kasafin Kudi ta Duniya IBP da Cibiyar binciken ‘kwakwaf da bayar da rahoto ta Duniya, ICIR.