On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Cikin Kwana 100 Rundunar 'Yan Sanda A Jihar Kano Ta Kama Mutane Sama Da Dubu 'Daya (1000) Bisa Zargin Aikata Laifuka

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mohammed Usaini Gumel, yace an kama mutane sama da dubu 1 da ake zargi da aika laifuka, tare da gurfanar da su a gaban kotu a cikin kwanaki 100 da ya yi da kama aiki.

Gumel ya bayyana haka ne a shalkwatar  ‘yan jarida ta jihar Kano a lokacin da yake bayyana nasarorin da ya samu a cikin kwanaki 100 da suka gabata, yayin wani taron manema labarai na musamman, wanda shugabannin kungiyar ‘yan jaridu reshen kafafen yada labarai suka shirya.

A cikin kwanaki 100 da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano ya fara aiki an kama sama da mutane dub 1, an binciki wadanda ake zargin tare da wasu adadi mai yawa daga cikinsu wadan har yanzu  ke gidan yari suna jiran shari’a bisa laifuka daban-daban da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane, satar shanu, kisan kai da  ‘yan daba da masu rike muggan makamai da masu  fataucin muggan kwayoyi.

Kwamishinan  ‘yan sandan ya ce cikin mutanen akwai ‘yan fashi da makami 117, masu garkuwa da mutane 25, barayin shanu 6, masu safarar mutane 17, wadanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyi 34, barayin motoci 18, barayin motoci su 27, barayin baburin adaidaitasahu 16, barayin babur mai kafa 2 s 58 sai  19 da ake zargi da damfara da  636 da ake zargin ’yan daba ne.