
Tsohon ministan lafiya a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan, Chief Gabriel Aduku ya zama sabon shugaban kungiyar tuntuba ta Arewacin kasar nan.
Sakataren kungiyar , Burka Zarma ne ya sanar da haka, yayin wani taron manema labarai a jiya, jim kadan bayan kammala wani zaman kolin kungiyar, wadda ta amince da Aduk a matsayin sabon shugaban ta.
Chief Gabriel Aduku ya karbi ragamar shugabancin kungiyar tuntuba ta Arewa daga hannun tsohon ministan aikin Gona, Chief Audu Ogbeh, wanda wa’adin shugabancinsa ya kare a watan Maris.
Zai rike shugabancin jam’iyyar nan da tsawon shekara ukku mai zuwa.