Babban bankin kasa CBN ya fitar da wasu matakai na ka’idojin mayar da tsofaffin takardun kudi na naira a rassan sa dake sassan kasa baki daya.
Babban bankin ya sanar da cewa za a bude tsarin ne daga yau Laraba 15 zuwa Juma'a 17 ga watan Fabarairu na 2023.
Bankin yace mayar da kudaden ba shiri ne na musanya kudi ba, kuma ba za’a baiwa mutum sabbin takardun kudi a madadin tsofaffin takardun kudin da ya mayar ba.
Maimakon haka, za a karɓi tsofaffin takardun tare da sanyasu a asusun da mutum zai bayar wajen cike Formdin mayar da tsohon kudin.
Yace za’a amince da wani mutjm na uku a tsakiya ba wajen mayar da Kudin sannan za’ayi matakan tantancewa.
A yau Laraba ne dai Kotun Koli tan an Najeriya zata saurari karar da gwamnonin Kaduna da Kogi da Zamfara suka shigar dake neman a hana CBN aiwatar da matakin daina amfani da Tsaffin takardun Naira da aka sauyawa Fasali.