Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya sha alwashin rushe duk bankin da suka ki karbar tsofaffin kuɗi tare da mayar da shi makaranta domin inganta Ilimi a jihar.
Ganduje ya yi wannan gargadi ne lokacin da ya ziyarci wuraren da aka ajiye kayayyakin tallafi na abinci da gwamnatin Kano ta sayo domin rabawa ga al’ummar da nufin saukakawa musu a mawuyacin halin da ake ciki.
Gwamna ya ce gwamnatin jihar kano bazata lamunci dabi'ar bankuna ba na kin karɓar tsofaffin kudi, wanda hakan ya jefa al’ummar Kano cikin tsananin yanayin Rayuwa da matsi.
Cikin jawaban Ganduje ya ce” zamu kwace lasisin bankin da yaki karbar tsofaffin kuɗin sannan mu rushe bankin kuma mu mayar da shi makaranta domin amfanin al’umma, kuma duk masu kasuwancin da suka ki karbar tsofaffin kuɗi to zamu rufe wurin”.
Yace sakamakon wahalar da ake ciki gwamnati ta sayo kayan abinci na miliyoyin nairori wadanda suka haɗar da shinkafa da taliya da man girki da nufin saukakawa al’umma wahalar da babban bankin Najeriya ya jefa mutane.
Ganduje ya kara da cewa tuni aka samar da kwamitin da zai raba kayan lungu da sako.
A nasa jawabin shugaban kwamitin kuma dan takarar mataimakin gwamnan Kano a jam’iyyar APC Murtala Sule Garo ya ce an siyo shinkafa buhu sama da dubu 90 sai masara dubu 22 sai taliya katan dubu 48 da kuma man jarka dubu 25.
Ya bada tabbacin cewa za su yi duk mai yiyuwa wajen ganin an raba kayan ga mabukata a kananan hukumomin jihar Kano domin rage musu radadi.