Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga 'yan kasa a yau Alhamis 16 ga Fabrairu, 2023 da karfe 7 na safe.
Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da Jama'a, Femi Adesina shine ya tabbatar da hakan ya cikin Wata sanarwa da ya fita a cikin daren da ya gabata.
Sanarwar ta umurci gidajen Talabijin da gidajen Rediyo da sauran kafafen yada labarai na zamani da su kasance da gidan Talabijin na kasa NTA da kuma gidan Rediyon tarayya domin shugaban kasar.
A kasance da tashar Arewa Radio mita 93.1FM ko ta Internet akan www.arewaradio.com daga ko'ida a duniya domin jin jawabin na shugaba Buhari ga 'yan Najeriya.