Babban bankin kasa CBN ya sha alwashin gurfanar da masu POS dake tsawwala chajin hada-hadar kuɗi ga 'Yan Najeriya.
Gwamnan bankin na CBN Emefiele ya yi wannan gargadi ne a wani taron tattaunawa da aka gudanar tare da karamin ministan kasashen waje a Abuja.
Emefiele ya amince da cewa duk da wadannan lokuta ne masu wahala ga ’yan Najeriya, bai kamata a yi karin kudi musamman daga masu ikon tafiyar da harkokin kuɗi domin haifar da tsanani ba.
Shugaban bankin ya nanata alfanun da aka samu biyo bayan sake fasalin kudi na Naira, yana mai cewa ta taimaka wajen rage hauhawar farashin kayayyaki da kuma kawo daidaito a farashin canji.
Emefiele ya yi kira ga jami’an diflomasiyya da ‘yan Najeriya da su amince da wannan tsari.
Ya yi nuni da cewa, duk da cewa bijiro da tsarin takaita zagayawar takardun kudi na Naira na iya zama kalubale, amma fa’idojinsa na da yawa kuma zai haifar da tsarin mai kyau ga harkokin kuɗi.
Shugaban na CBN ya kafe akan cewa babu gudu babu ja da baya akan ranar 10 ga watan Fabrairu matsayin ranar daina amfani da tsohon kudi.
A cewarsa, tattalin arzikin kasa zai fuskanci abin da ya kira ci gaba sosai.
A nasa jawabin, Karamin Ministan Harkokin Waje Zubair Dada ya bayyana cewa taron ya zama wajibi a wani bangare na kokarin sanar da manufofin tattalin arziki na gwamnati dangane da sake fasalin Naira.