On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Canada Ta Bada Tallafin Naira Billiyan 2.6 Domin Karfafa Shigar Da Mata Harkokin Siyasa A Najeriya

Gwamnatin Canada ta ba da gudummawar zunzurutun kudi har naira biliyan 2 da milliyan dari 6 domin ci gaban mata a harkokin siyasa a Najeriya.

Babban jakadan Kanada a Najeriya, James Christoff shine ya bayyana haka a Abuja ranar Litinin, yayin wata tattaunawa da shugabannin gargajiya, wanda ofishin jami’an Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya da offishin mata na majalissar suka shirya.

Tattaunawar ta manyan jami'an Majalisar Dinkin Duniya na neman jawo hankalin shugabannin gargajiya da su kara kaimi wajen kawo karshen cin zarafin mata a kasarnan.

Christoff, wanda Ms Djifa Ahado, shugabar hadin gwiwa, a ofishin jakadancin Canada a Abuja, ta wakilta, ta bayyana cewa za a bayar da kudaden ne na tsawon shekaru hudu a karkashin wani shiri na neman shigar da karin mata cikin siyasa a Najeriya na kasar Canada.