Burtaniya na shirin zama daya daga cikin manyan kasashe mafi tabarbarewar tattalin arziki a bana, a cewar bada asusun lamuni na duniya IMF.
Asusun ya baiyana cewar tattalin arzikin Birtaniya a shekarar 2023 zai kasance mafi muni a cikin manyan kasashe 20 masu karfin tattalin arziki, da aka fi sani da G20, wanda ya hada da kasar Rasha da aka kakabawa takunkumi.
Asusun na IMF ya yi hasashen tattalin arzikin Burtaniya zai ragu a wannan shekara.
Hakan ya biyo bayan faduwar wasu bankunan Amurka guda biyu a watan da ya gabata, bayan da Bankin UBS da suke gogagga dashi ya yi gaggawar kwace babban bankin kasar Switzerland , lamarin da ya kara haifarwa kasar ta burtaniya dagulewar lamura.