‘Dan takarar jam’iyyar Labour a zaben shugaban kasa na 2023, Peter Obi ya ce burinsa na ganin sabuwar Najeriya bai kare ba, duk da kotun koli ta yanke hukunci a ranar 26 ga watan Oktoba da ya gabata.
Obi ya yi magana ne a wani taron manema labarai a Abuja kimanin makonni biyu bayan kotun kolin ta tabbatar da nasarar zaben shugaban kasa Bola Tinubu a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Obi, wanda ya caccaki hukuncin da kotun kolin ta yanke, ya amince da cewa an kawo karshen shari’ar zaben da ya gabata.
Ya ce har yanzuyana nan akan barkarsakuma gwiwarsaba zata yi sanyi ba.
Ko da yake bai fito fili ya bayyana ko zai sake tsayawa takarar Shugaban kasa a 2027 ba, ya ce ba a kawo karshen tafiyarsa ta neman samar da sabuwar Najeriya ba.