Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da sabuwar matatar mai ta Dangote a yau Litinin, wadda ake sa ran zata tace gangar mai dubu 650 kowacce rana domin rage wahalar shigo da tacaccen mai cikin kasarnan.
Ana sa ran wannan matata ta dinga tace man fetur da man dizil da kalanzir da kuma man jiragen sama, matakin da ake ganin zai rage matsalolin da ake fuskanta yanzu na rashin samun wadataccen man da ake tacewa a cikin gida.
Da yake magana game da katafaren kamfanin, shugaban matatar man ta Dangote, Sanjay Gupta, ya ce matatar wadda ita ce mafi girma da wani ‘dan kasuwa ya mallaka a nahiyar Afirka, kuma wadda ake sa ran ta samar da kasuwar da ta kai Dala biliyan 21 kowacce shekara wajen sayan danyan mai daga hannun gwamnatin Najeriya.
Bayanai sun ce a makwanni masu zuwa ake saran kamfanin ya fara aiki gadan gadan.
Ana sa ran kaddamar da wannan matatar mai a jihar Legas.