On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Buhari Ya yi Allah Wadai Da Yawan Harin Ta’addanci a Kudu Maso Gabashin Najeriya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kashe-kashen dake faruwa a Kudu-maso-Gabas, Ya kuma roki Jama'a su ba da bayanai da zasu taimakawa hukumomi.

 

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu ya sanyawa hannu a ranar Asabar, Buhari ya sha alwashin daukar dukkan matakan da suka dace wajen gudanar da bincike cikin gaggawa domin gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya.

Martanin shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa an kashe wasu ‘yan kasar Nijar shida da kuma kisan gilla da aka yi wa wasu ‘yan sanda a wuraren aikinsu.

An kashe jami’an ‘yan sanda hudu a Imo ranar Asabar bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari ofishin ‘yan sanda.

Shugaban ya bukaci shugabannin al’umma da na addinai da su kara kaimi wajen wayar da kai kan bukatar tabbatar da zaman lafiya.