Shugaban kasa Mohammadu Buhari ya bukaci gwamnan babban bankin kasa na CBN, Godwin Emefile da ma sauran jami'an gwamnatin sa dake da burin tsayawa takara a zabe mai zuwa da su sauka daga mukaman su ba tare da wani bata lokaci ba.
Umarnin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Boss Mustapha ya sanyawa hannu a safiyar ranar Alhamis.
Shugaban babban bankin na kasa na daya daga cikin wadanda aka turawa kwapin umarnin mai taken "Ministoci, Shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnati, da jakadu masu niyyar tsayawa takara su sauka daga mukaman su".
"Shugaban kasa ya fahimci cewa akwai mambobi na majalisar zartarwa ta kasa, shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnati, jakadu da sauran masu rike da mukamai na siyasa da suka yanke shawarar tsayawa takarar neman mukamai daban-daban a fadin kasar nan".
"Bisa wannan dalili ne shugaban kasa ya umarci dukkan jami'an gwamnati dake da niyyar tsayawa takara da su gabatar da takardun ajiye aikin su kafin ko kuma ranar Litinin, 16 Mayu 2022".
"Domin kade shakku, wannan sanarwa ta shafi daukacin ministoci, shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnati, jakadun Najeriya a kasashe daban-daban, da ma sauran masu rike da mukaman siyasa dake son tsayawa takara a zabe mai zuwa".
"Domin cigaba da gudanar da aiyukan gwamnati yadda ya kamata, shugaban kasa ya umarci ministoci da su danka ragamar shugabanci a hannun kananan ministocin su idan da akawai, kuma manyan sakatarorin ma'aikatun. Hakan nan, sauran shuwagabbin hukumomin zasu mika ragamar gudanarwar ne ga jami'an su mafiya girman mukami.
Shugaban babban bankin kasa na CBN, Godwin Emefile na daga cikin wadanda suka fi fuskantar matsin lamba kan kiraye-kirayen ajiye mukami ga jami'an gwamnati dake da burin tsyawa takara a zabe mai zuwa.
Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, yayi kira ga shugaba Buhari da ya tsige gwamnan babban bankin na kasa, tunda ya ki sauka bisa radin kansa.
Ita ma babbar jam'iyyar hamayya ta PDP, a baya-bayannan cewa tayi kamata yayi a kama gwamnan babban bankin kasar saboda manufar sa a zabe mai zuwa da kuma kin yadda ya sauka daga mukamin sa da yayi.