Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi daga filin jirgin saman Azikiwe dake Abuja domin halartar bikin nadin sarautar Sarki Charles na uku da aka shirya yi a karshen makon nan.
Gabanin nadin sarautar, sakatariyar Kungiyar kasashe renon Ingila za ta yi amfani da damar taron shugabannin da za a yi a birnin Landan domin karbar bakuncin taron koli na shugabannin gwamnatocin kasashe mambobin kungiyar a ranar Juma'a 5 ga watan Mayun da muke ciki.
Shugaban kasar ya yi balaguro ne tare da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha da Ministan Harkokin kasashen Waje, Geoffrey Onyeama sai Ministan Yada Labarai da raya Al’adu Lai Mohammed da mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno.
Sauran sun hada da Shugaban hukumar leken asiri ta kasa, Ambasada Rufai Abubakar da shugabar hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Uwargida Abike Dabiri-Erewa, da sauran manyan jami’an gwamnati.