Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami Sakatariyar Zartaswa kuma Babbar Jami’ar Hukumar Bunkasa Zuba Jari ta Najeriya Saratu Umar daga bakin aiki.
Matakin ya fara aiki nan take, acewar mai taimaka wa shugaban kasa Femi Adesina a wata gajeriyar sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
A cikin umarnin da ya baiwa Ministan Masana’antu, Ciniki, da Zuba Jari, Richard Adebayo, Shugaban ya kuma umarci babban Darakta a Hukumar da ya gaggauta karbar ragamar aiki na wucin gadi.
Tun a watan Yulin 2014 ne gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan ta nada ta amma ta kore ta a shekarar 2015.
A ranar 5 ga Yuli na 2022, Shugaba Buhari ya nada ta wa'adin shekaru biyar.