Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka hannu kan kasafin kudin bana wanda ya kai naira tiriliyan 21 da bilyan 83 da kuma kwarya-kwaryar kasafin kudin shekarar data gabata.
A lokacin da yake saka hannun kan kasafin kudin, Shugaban kasa Buhari ya baiyana cewa an yiwa kunshin kasafin kudin karin naira tiriliyan 1 da bilyan 32, akan ainihin alkaluman kasafin kudin na farko da bangaren zartawa ya gabatarwa majalisar dokoki ta kasa, wanda ya kama naira tiriliyan 20 da bilyan 51.
Dangane da kwarya-kwaryar kasafin kudin shekarar data gabata kuwa, Shugaban kasar, ya baiyana cewa , amincewa dashi zai baiwa gwamnatinsa damar daukar matakan da suka dace na yin gyararrarki akan barnar da aka samu sakamakon ambaliyar ruwa data afkawa bangaren aikin gona.
Ya kara da cewa, ministar kudi kasafi da kuma tsare-tsaren cigaban kasa zata yi cikakken bayani akan kunshin kasafin kudin, wanda zai yi aiki tare da tallafin dokar kudi ta shekarar 2022.