Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin a lokacin da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar PDP a jihar Kano
Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya ce afuwar da shugaban kasa ya yi wa mutanen da gwamnatin tarayya ta tuhume su da laifin cin hanci da rashawa ya nuna cewa babu bukatar a samu hukumomin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.
Wike Ya yi amanna cewa hukumar yaki da masu yi wa tattalin Arzikin Kasa zagon Kasa ta EFCC da kuma ICPC sun fuskanci abin kunya saboda yafiyar da akayi musu bata da wani muhimmanci.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin a lokacin da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar PDP a jihar Kano, a ci gaba da tuntubar da yake yi gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.
Ya na mai da martani ne kan afuwar da majalisar magabatan kasarnan ta yiwa tsoffin gwamnonin jihar Taraba Jolly Nyame da Joshua Dariye na jihar Filato a makon jiya. .