Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiyana cewa makaman da ake amfani dasu a yakin da ake gwabzawa tsakanin kasar Rasha da kuma Ukrain, sun fara kwarorowa yankin kasashen Afrika, musamman ma yankin tafkin Cadi.
Shugaban kasar ya baiyana haka ne a yayin taron shugabannin kasashen yankin Tafkin Chadi karo na 16 a Abuja.
Buhari wanda shine shugaban taron, Lamarin wanda ya kara ta’azzara karuwar bazuwar kanana da kuma manyan makamai, na bukatar sake inganta matsaron da ake dasu akan iyakokin kasashen.
Ya kara da cewa yakin Kasashen Rasha da Ukrai, da sauran wasu kasashen dake fama da rikici a yankin Sahel na yammacin Afrika, ya kara temakawa kungiyar Mayakan Boko Haram wajen samun wurin zama a yankin tafkin Chadi.