Shugaban Kasa Muhammadu Bihari, ya kaddamar da wasu manyan ayyuka a jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya.
Ayyukan sun hada da, bude kwalejin horas da sojojin ruwa, a Karamar hukumar Dawakin Tofa ( Nigerian Navy Logistics college) sai katafaren gidan gyaran hali na Janguza da kuma gyara da aka yiwa filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano ( MAKIA) inda aka samar da sabon Sashen Tashi Da Saukar Jiragen Sama Na Kasashen Ketare
An kaddamar da wandan ayyuka ne ta allon-gani-ga-ka.
Shugaban ya yabawa gwamnan jihar da kuma hafsan sojin ruwa Vice Admiral AZ Gambo bisa kokarinsu na ganin an kammala aikin da kuma tabbatar da nasarar aiwatar da dukkan ayyukan.
A nasa jawabin, Ministan Tsaro, Janar Bashir Salihi Magashi, ya ce kwalejin ta yaye dalibai sau biyu, kuma za ta yaye na uku a wata na shida nan gaba, inda ya ce kwalejin na neman sahalewa daga hukumar kula da ilimin fasaha ta kasa domin a fara karatun Diploma da shaidar HND a wasu kwasa-kwasai, inda farar hula zasu fara karatu a kwalejin.
Shi kuwa gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya yabawa shugaban Kasar bisa wadannan muhimmanci ayyuka da shugaban Kasar ya gudanar a jihar Kano.