Bayan kammala wa'adin shekara 8 Muhammadu Buhari ya zama tsohon shugaban Najeriya
Bayan mika mulki ga Tinubu Buhari da 'yan tawagarsa sun fice daga filin taron rantsuwa cikin ayarin motoci.
Tuni aka tsaurara matakan tsaro a garin Daura, mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari mai barin gado, gabanin komawarsa bayan rantsar da zababben shugaban kasa a yau.
Buhari zai koma Daura bayan mika mulki ga sabon shugaban kasa a Abuja.
Za a kai shi Katsina daga Abuja daga bisani kuma a kai shi Daura a wannan rana.
A fadar sarkin Daura, an sanya alluna a bakin kofar da ke dauke da sakonnin da ke cewa shugaban ya yi nasarar kammala wa’adinsa kuma ya yi wa kasa hidima.
Haka kuma garin yana karbar baki saboda babu ragowar daki a otal din Daura Motel wanda ya kasance daya tilo da ke Daura.