Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bada takardar daukar aiki kai tsaye ga wasu masu aikin hidimtawa kasa guda 65.
Da yake jawabi a wajen bukin cika shekara hamsin da kafa hukumar kula da shirin masu hidimtawa kasa a dakin taro na fadar shugaban kasa dake Abuja, Shugaban kasar ya baiyana irin dimbin nasarorin da aka samu a sakamakon bijiro da shirin shekara hamsin da ta gabata.
Shugaban kasar ya baiyana cewar, Daga cikin mutanen da aka dauka aiki, An kuma karrama wasu guda 52 da lambobin karramawa, Yayin da guda 13 da suka kasance masu bukata ta musamman zasu ci gajiyar shirin bada jari dake karkashin hukumar ta NYSC.
Bugu da kari, Shugaban kasar ya baiyana cewar , za’a kuma baiwa mutanen tallafin karo karatu domin cigaba da gudanar da karatunsu a jami’ar da suka zaba cikin kasar nan.