On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Buhari Ya Amince Da Karawa 'Yan Najeriya Wa'adin Kwana 10 Su Chanja Tsohon Kuɗi Zuwa Sabo

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da tsawaita wa'adin kwanaki 10 na chanjin tsaffin kudade zuwa sabbi da aka sauyawa fasali.

Kamfanin dillancin labaru NAN ya rawaito cewa gwamnan babban bankin Najeriya CBN, wanda ya tabbatar wa manema labarai hakan a garin Daura na jihar Katsina, ya bayyana cewa sabon wa'adin zai kare a ranar 10 ga watan Fabrairu. 

Emefiele, wanda ke Daura a safiyar Lahadi, ya yi ganawar sirri da Buhari a garin na daura dake Jihar Katsina, inda ya samu amincewar karin wa'adin. 

Yace ’yan Najeriya, wadanda har yanzu ba su canza tsaffin kudinsu na Naira ba, yanzu suna da damar yin hakan.

 Gwamnan babban bankin ya yi gargadin cewa dole ne mutane su yi amfani da damar domin ba za a sake tsawaita wa'adin ba.

Idan za'a iya tunawa dai CBN ya tsayar da ranar 31 ga watan Janairu a matsayin wa’adin daina amfani da  tsaffin takardun kuɗi na  Naira da aka sakewa fasali.

Kudin Naira da aka sakewa fasali, wanda ya hada da Naira 200 da Naira 500 da kuma Naira Naira 1,000 sun zama doka a ranar 15 ga Disamba na shekarar 2022, bayan Buhari ya kaddamar da su a ranar 23 ga Nuwamba na  2022 a Abuja.

Rahotannin daga sassan Najeriya a  ranar Asabar sun nuna cewa ‘yan kasuwa na bukatar kwastomominsu da su biyasu da sabbin takardun kudin. 

An kuma gano cewa har yanzu wasu daga cikin na’urori cire  kudi na ATM a fadin jihohi ciki har da babban birnin tarayya Abuja, suna ci gaba da bada tsofaffin takardun kudin Naira, yayin da ake samun dogayen layukan a  na’urar ATM  da ke bada takardun kudin na Naira da aka sakewa fasali. 

Wasu bankunan da ke ba da sabbin takardun kudin suna bada abunda bai wuce  Naira dubu 5  ko dubu 10 ba a kowane cirewa.

 Har ila yau, wasu cibiyoyin POS na ci gaba da bada   tsofaffin takardun kudin na Naira.