Shugaba Mohammadu Buhari ya zargi wasu kasashen duniya da yunkurin ruguza Najeriya ta hanyar daukar nauyin ayyukan masu tada kayar baya a fadin kasarnan.
Da yake jawabi a Kano bayan kaddamar da ayyuka 8, Buhari yace duk da cewa mutane suna da mantuwa, amma gwamnatinsa tayi nasarar ceto kananan hukumomi da dama a jahohin Borno da Yobe daga hannun ‘yan ta’adda....
Da yake magana kan tabarbarewar tattalin arzikin kasa, shugaban ya yi ikirarin cewa idan aka kwatanta da halin da ake ciki a wasu kasashen dole ne 'yan Najeriya su koyi sanin kima da girman kasarsu.
Shugaban ya ce ‘‘muna da ƙasaitacciyar ƙasa, amma ba ma yaba mata, har sai mun ziyarci ƙasashe maƙwabta da sauran ƙasashe, inda sai mutane sun yi da gaske sannan su sami abinci sau ɗaya a rana''.
‘‘A lokacin da nake shawagi a cikin jirgi adadin dogayen gine-ginen da na gani da yawan ci gaban da ake da shi a doron ƙasa abin ' ban sha'awa' ne. Mun gode wa Allah, Mun gode wa Allah'', in ji Buhari.
Shugaban ƙasar ya kuma umarci manyan 'yan ƙasar da su ƙarfafa wa matasa gwiwwa wajen rungumar ilimi, yana mai cewa dole ko ana so, ko ba a so makomar ƙasar a hannun matasan take.
Ya ce '‘dole su rungumi ilimi, Fasaha ta saukaka abubuwa da dama, to amma babu abin da zai maye gurbin ilimi, dan Allah ku ƙarfafa wa yara gwiwwa su samu ilimi''.
Daga nan sai ya yabawa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa gagarumin cigaban ababen more rayuwa da ya samar.