On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Buhari Da Mataimakinsa Zasu Kashe Sama Da Naira Bilyan 3 Wajen Yin Tafiye-Tafiye

SHUGABA BUHARI ZAI SHIGA JIRGI

Fadar shugaban kasa, Ta yi kiyasin cewa jimillar tafiye-tafiyen cikin gida dana kasashen waje da shugaban kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo zasu yi a shekarar 2023, zasu lakume zunzurutun kudi har naira milyan dubu 3 da Milyan 34, kamar yadda bayanan hakan ke kunshe cikin daftarin kasafin kudin Badi, da shugaban kasar ya gabatar ranar juma’a a gaban zauren majalisar dokoki ta kasa.

Daga cikin naira bilyan 2 da milyan 49 da shugaban kasar zai kashe a bangaren  balaguro, Naira milyan 862 zasu tafine bangaren  tafiye-tafiye na cikin gida, yayin da balaguron kasashen ketare, zasu lashe naira bilyan 1 da milyan  600.

Kazalika kiyasin kudin tafiye-tafiyen da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbanjo zai kashe a badi, sun kama narai milyan 846, inda bangaren balaguron cikin gida zai ci naira 330 a yayin da na kasashen waje zai ci sama da naira milyan 5116.

Kasafin kudin na badi ya nuna cewa fadar shugaban kasa da sauran hukumomin dake karkashin fadar zasu kashe sama da naira bilyan 133 da milyan 730 da dubu 697 da naira 750, ta bangaren  gudanar da aiyukan yau da kullum, da kuma manyan aiyuka da sauran yan kunji-kunji.