Muddin ba’a samu wani sauyi ba, zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu na iya dawowa Najeriya a yau Litinin.
A ranar 21 ga watan Maris ne Tinubu ya yi balaguro zuwa birnin Paris da Landan domin ya huta da kuma tsara shirin karbar mulki gabanin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.
Sakataren yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, James Faleke, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, ya ce jirgin saman Tinubu tare da matarsa, Sanata Remi Tinubu, zai sauka a Abuja da karfe 2 na rana.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake takaddamar shugabanci majalisun wakilai da Dattijai, kuma ake saran Tinubu zai nuna tsarin da za’abi wajen fitar da jagorancin majalissun.