Gwamnatin Tarayya na neman biyan mafi karancin albashi daga kamfanoni masu zaman kansu na sauran matakan gwamnati gwamnati domin tabbatar da cewa ma’aikata ba su shiga cikin wani hali ba.
Gwamnati ta dage cewa aiwatar da mafi karancin albashi na Naira dubu 30 na da matukar muhimmanci ga ci gaban kasa.
Ministan kwadago da ayyukanyi, Dakta Chris Ngige shine ya bayyana hakan a wajen taron wayar da kan jama’a da ke sa ido kan yadda ake aiwatar da mafi karancin albashin ma’aikata a Abuja.
Ngige yace bangarorin gwamnati da wadanda ba na gwamnati ba sun samu wakilci sassan a lokacin fitar da tsare-tsaeen da suka samar da dokar, saboda haka babu wani bangare da zai iya ikirarin rashin akan tsarin.