Hukumar Korafe-korafe da yaki da cin hanci da Rashawa ta Jihar Kano, ta ce binciken kwakwaf ya tabbatar da cewa faifan bidiyon dala na tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje na gaskiya ne, ba hadawa akayi ba.
Shugaban Hukumar Muhuyi Magaji Rimingado ya tabbatar da sahihancin faifan bidiyon a wajen wani taron tattaunawa na kwana daya kan yaki da cin hanci da rashawa da aka gudanar a Kano ranar Laraba.
Ya ce hukumar ta fara bincike a shekarar 2018 amma ta gaza cigaba da aiwatarwa saboda Ganduje da ya ke gwamna a lokacin yana da kariya.
Idan za’a iya tunawa shekarar 2017, wata kafar yada labarai ta Internet, Daily Nigerian, ta fitar da wasu faifan bidiyo na Ganduje da ake zargin yana karbar cin hanci daga hannun ‘yan kwangila.