Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu ya ce ko a jikinsa, irin kiraye-kirayen da wasu suke yi cewa ya sauka daga kan mukaminsa.
Yace masu yin kiraye-kirayen yara ne da ba su fahimci manufofin kafa jam’iyyar ba.
A zantawarsa da kafar yada labarai ta BBC, shugaban jam’iyyar wanda ya kasance tsohon dan Majalisar Dattawa, ya ce a iya saninsa ‘yan Najeriya ne suka zabe shi bisa sharuddan da jam'iyyarsu ta shimfida.
An jima ana kai ruwa rana tsakanin jam'iyyar da dan takarar shugaban kasa da ya sha kaye a hannun Atiku Abubakar a zaben fid da gwani, gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, wanda rahotanni suka ce ya gindaya sharuddan ci gaba da zama a jam'iyyar, da kuma mara wa Atiku Abubakar baya a matsayin dan takararta a zaben 2023.
Daga cikin sharuddan akwai bukatar Shugaban jam'iyyar Iyorchia Ayu, wanda ya fito daga Arewacin kasarnan ya sauka daga mukaminsa.
Sai dai Mr Ayu ya ce ba bu inda za shi, la'akari da cewa an zabe shi ne bisa dokokin da jam'iyyar PDPn ta shimfida, a don haka ba zai sauka ba saboda kawai wasu ba sa son ganin shi a kai.
Haka kuma ya musanta batun cewa rashin dinke baraka da Gwamna Wike zai iya kawo wa jam'iyyar cikas a zaben na 2023, inda yace su suka asassa jam'iyyar PDP a Najeriya, saboda haka 'wasu yara' da ba su san gwagwarmayar da suka sha ba ba za su iya basu matsala ba.