On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Bazan Juyawa 'Yan Takararmu APC Baya Ba - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce har yanzu shi dan jam’iyyar APC ne mai da'a kuma a  zabe mai zuwa ba zai goyi bayan wasu ‘yan takara ba sabanin ‘yan takarar da jam’iyyar ta tsayar a kowanne mataki.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar jiya a Abuja.

Shugaban na ya kuma gargadi ‘yan jam’iyyar da suka sauya sheka da wasu da har yanzu suke gaban kotu kan ‘yan takarar jam’iyyar APC da cewa suna yin hakan ne bisa radin kan su , kuma babu wanda ya isa ya danganta abin da suke yi da shi.