Kungiyar kwallon kafa ta Wolves ta kori mai horas da 'yan wasanta Bruno Large, sakamakon rashin nasara a hannun West Ham a gasar Premier a ranar Asabar.
Wasa daya kacal kungiyar Wolves ta ci da rashin nasara a tara daga cikin wasanni 15 da ta buga a baya a gasar Premier, karkashin mai horaswar dan kasar Portugal.
Lage ya maye gurbin Nuno Espirito Santos ya kuma kai kungiyar mataki na 10 a kakar farko da ya ja ragama. sai dai Wolves ta ci kwallo uku kadai a bana da hada maki shida daga karawa takwas a gasar Premier.
Kungiyar ta kashe kudi sama da £100m wajen sayo 'yan wasa a kakar wasa ta bana, domin ta kara azama fiye da wadda ta yi a shekarar da ta gabata.
Ta dauko dan wasan Portugal, Goncalo Guedes da Matheus Nunes, kowanne kan £38m a matakin mafi tsada a kungiyar da ta saya a tarihi..
Wolves ta fada matsala, bayan Sasa Kalajdzic da Raul Jimenez suka ji rauni a kakar bana.
Magoya bayan kungiyar sun yi wa 'yan wasa ihu, bayan da West Ham ta doke Wolves a karshen makon jiya.