A karon farko Darasin Tarihi ya zama darasi mai cin gashin kansa a cikin manhajar ilimi ta Najeriya bayan shafe shekaru 13 da cire darasin.
Gwamnati ta nunar da cewa malaman Tarihi dubu 3 da 700 ne aka zaba domin horas da su a rukunin farko domin inganta koyarwa a fannin.
Gwamnatin tarayya ta sanar da sake dawo da darasin a hukumance.
Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da manhajar a Abuja, Ministan ilimi, Adamu Adamu ya koka da yadda hadin kan kasa ke fuskantar barazana.
Adamu ya kara da cewa kasarnan na komawa cikin wani yanayi na kiyayya mara amfani tun bayan cire Tarihi daga cikin manhajar ilimi.
An cire tarihi daga manhajar karatun firamare da sakandare daga zangon karatu na 2009/2010.