Hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta kasa ta cire sunan Hajiya Naja’atu Mohammed, a matsayin ɗaya daga cikin masu sanya idanu na hukumar da za su lura da ayyukan 'yan sanda a yankin arewa maso yamma lokacin babban zaɓen da ke tafe.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce an jawo hankalinta ne kan wata sanarwa da jam'iyyar APC mai mulki ta fitar, inda ta yi zargin cewa Hajiya Naja'atu na goyon bayan wata jam'iyya saboda haka APCn take gani ba za ta yi wa jam'iyyar adalci ba.
Sanarwar da hukumar 'yan sanda ta fitar ta ce ta maye gurbinta da tsohon mataimakin babban sifeton 'yan sanda Bawa Lawan domin lura da ayyukan 'yan sanda a shiyyar ta arewa maso yamma.
‘Yar siyasar haifaffiyar jihar Kano ta sha sukar jam’iyyar APC da dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu, bayan ta fice daga jam’iyyar domin marawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar baya.
Tunda farko dai, majalisar yakin neman zaben jamiyyar APC yaki amincewa da nadin Naja’atu Bala Muhammad a matsayin jami’ar gudanarwar a harkokin yan sanda a yankin arewa maso yammaci a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu dana 11 ga watan maris din dake tafe.
Mai mgana da yawun majalisar yakin neman zaben jamiyyar APC Festus Keyamo SAN ta cikin wata sanarwa da aka fitar a yau yace a dakatar d it aba tare da bata lokaci ba.