Babban mai taimakawa shugaban majalisar dattawan kasarnan sanata Ahmed Lawan kan harkokin jama'a Alhaji Bashir Hayatu Abubakar ya yi murabus daga mukaminsa a ranar Alhamis.
Fitaccen masanin harkokin siyasa kuma mai fashin baki, Bashir Hayatu Abubakar wanda aka fi sani da Jantile ya sanar da yin murabus daga mukaminsa a wata wasika da ya aikewa shugaban majalisar dattawa kuma ya rabawa manema labarai.
A cikin kwafin wasikar da Arewa Radio ta samu, Hayatu Jantile, ya ce ya yi murabus daga mukaminsa na Babban mai ba da shawara kan harkokin jama’a ga shugaban majalissar bisa dalilai na kashin kai.
A cikin wasikar mai kwanan watan jiya Alhamis 22 ga Disamba, 2022, Bashir Jantile ya shaida wa shugaban majalisar dattawa cewa, murabus din ya fara aiki daga 1 ga Janairu na shekarar 2023 da ke tafe.
Daga nan sai Bashir Jantile ya godewa shugaban majalisar dattawan da ya ba shi damar yin wannan aiki, inda ya bukaci da ya kara yi masa jagora da addu’a da kuma goyon baya a sauran harkokinsa ko ayyukansa na nan gaba.