
A karon farko kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta lashe gasar La Liga tun bayan daga kofin a shekarar 2019, bayan da ta lallasa Espanyol da ci 4 da 2 a wasan da suka fafata a ranar Lahadi, inda ta yi fafutikar karbe kanbun gasar daga hannun Real Madrid.
Kungiyar ta yankin Catalonia ta lashe gasar ne a karo na 27, Sai dai kuma daga bisani wasu mutane da suka yi dirar ba zata cikin filin wasan,sun rika korar magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da suke murnar lashe gasar.
Ita kuwa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta yi bankwana da gasar Firimiya bayan da Brighton ta casa ta da ci 3 da nema.
Daga karshe Manchester City ta lallasa Everton da ci 3 da nema.