On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Bankin Duniya Ya Ware Kudi Naira Billiyan 1.8 Domin Gyara Makarantun Gwamnati 614 A Jihar Kano

Wani shirin Inganta rayuwar yara mata ta hanyar Ilimi dake samun tallafin bankin duniya, ya ce zai gyara makarantun sakandire na gwamnati guda 614 a kan kudi Naira biliyan 1 da milliyan dari 8 a jihar Kano.

Mataimakin babban jami’ain kungiyar, Malam Nasiru Abdullahi shine ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci sauran ma’aikatan kungiyar suka kai ziyarar ban girma ga mai martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado-Bayero, a ranar Alhamis.

Ya ce tuni aka sanya  kudaden a asusun ajiyar bankunan kwamitocin kula da makarantun da zasu amfana.

A nasa jawabin, mai martaba sarkin na Bichi Alhaji Nasiru  Ado-Bayero ya yi alkawarin bayar da goyon baya tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki a harkar ilimi da su kara bada himma  wajen inganta kwazon malamai.

Sarkin ya kuma bukaci jama’a da su daina janye ‘yan mata daga makarantu domin aurar da su, yana mai rokon kada a dakatar da karatun ‘yan matan a matakin sakandare kawai.