Bankin Duniya ya ce har yanzu gwamnatin tarayya na iya biyan tallafin man fetur kasancewar har yanzu farashin man fetur a kasar nan bai yi tsadar data wuce makadi da rawa ba.
Babban masanin tattalin arziki na Bankin Duniya a Najeriya, Alex Sienaert, ya tabbatar da ci gaba da biyan tallafin man fetur da gwamnati ke yi a Abuja, yayin gabatar da jawabinsa a wajen wani taron mahangar cigaban kasar na watan Disambar da muke ciki.
Ya ce har yanzu farashin man fetir a kasar nan bai yi daidai da yanayin kasuwar mai ta duniya ba, inda y ace kamata ya yi farashin litar man ta kai naira 750 a maimakon naira 650 da ake siyar da ita a halin yanzu.
Wannan tsokaci na zuwa ne , yayin da ‘yan Najeriya da dama suka ajiye motocinsu sakamakon tashin gwauron zabo da suka ce farashin na Man fetir ya yi, sannan kuma aka samu tashin kayan masarufi, biyo bayan karin farahin man fetir da aka yi, wanda ke kamawa tsakanin naira 650 zuwa 700 akan kowacce lita daya.