Kwamitin ayyuka na musamman na majalisar dattawa ya gayyaci ministar kudi da kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed kan sanya kudi naira biliyan 206 a cikin kasafin kudin shekarar 2023 na ma’aikatar jin kai.
Shugaban kwamitin Sanata. Yusuf Yusuf shine ya sanar da hakan a lokacin da ministar harkokin jin kai, Sadiya Farouq, ta bayyana gaban kwamitin a ranar Litinin domin kare kasafin.
An tambayi ministar akan kimanin Naira biliyan 206 a cikin kasafin kudin da ta yi niyyar ciyo bashi. Nan take ta ba da amsar cewa an gabatar da irin wannan adadi a kasafin kudin shekarar 2022 amma ba a saki kudaden ba.
Sai dai ta musanta masaniya game da yadda adadin ya sake kunno kai a cikin kasafin kudin shekarar 2023 da ake shirin yi, al’amarin da ya sa kwamitin ya gayyaci ministar kudi domin amsa tambayoyi.