Injiniya Sani Bala ya ce majalisar Wakilai nada tarin dalilai na dakatar da aiwatar da karin kudin wutar lantarkin.
Majalisar wakilai ta ce ta dakatar da yunkurin hukumar kula da harkokin Lantarki ta kasa na yin Karin kudin wutar lantarki a wannan lokaci, saboda Karin zai cutar da Talakawan Kasa.
Majalisar ta ce Karin kudin wutar cike yake da sarkakkiya a saboda haka ne ta bukaci a dakatar da aiwatar dashi.
Dan Majalisar wakilai na Ghari da Tsanyawa engr Sani Bala Tsanyawa ne ya baiyana haka a yayin hirarsa da Arewa radio.
Ya kara da cewar samar da cibiyoyin ruwa da tashoshin nukiliya a Kasar nan, zasu taka muhimmiyar tawa wajen magance matsalar karancin wutar lantarki a Kasar nan.
Ya ce akwai aiyukan bunkasa samar da Lantarki da aka yi watsi da su tun a tsaffin gwamnatocin baya, da ya Kamata a farfado dasu domin inganta samar da Lantarki.