Jam’iyyar NNPP ta musanta duk wani yunkuri na ruguza tsarinta domin narkewa cikin wasu jam’iyyun siyasa.
Shugaban jam’iyyar na kasa Farfesa Rufa’i Alkali, ya ce jam’iyyar bata shirya mika kanta a matsayinta jam’iyyar siyasa mai rijista ga wata jam’iyya ba.
Alkali wanda ya zanta da manema labarai a jihar Legas, yana mayar da martani ne kan rade-radin da ake yi na cewa magoya bayan dan takararta na shugaban kasa kuma jagoran jam’iyyar na kasa, Sanata Rabiu Kwankwaso na tattaunawa da dan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Da yake mayar da martani kan batun, shugaban na NNPP, ya ce tuni suka rufe kofar hadaka tsakanin jam’iyyun siyasa.
...