On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Bama Goyon Bayan Kudirin Rancen Kudin Karatu Ga 'Dalibai A Najeriya - ASUU

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa ASUU, ta bukaci Majalisar Wakilai ta yi watsi da kudirin neman bada rancen kudi ga dalibai, inda ta ce matakin zai kara haifar da matsaloli.

Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana matsayin kungiyar kan shirin a rana ta biyu a taron koli na sake fasalin manyan makarantu na kasa a Abuja.

Farfesa Osodeke ya soki shawarar kudin makaranta ya koma Naira dubu 250 a kowane zangon karatu, inda dalibai za su nemi rancen Naira dubu 500 don biyan kudin  da kuma ciyar da kansu.

A cewarsa, a halin yanzu da ake fama da rashin aikin yi a kasarnan, zai yi wuya dalibai su iya  biyan irin wannan lamuni bayan kammala karatunsu.