Hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta kasa NCC ta musanta zargin bin diddigin da daukar maganganu da tattaunawar da Mutane ke yi ta wayar tarho, inda ta ce ba ta kuma ba za ta iya aiwatar da hakan bisa doka.
Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar NCC, Reuben Muoka, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya bayyana cewa hukumar ta samu sakonni kan ikirarin da wasu mutane da kungiyoyi ke yi na bibiyarsu ta wayar tarho da kuma daukar maganganun inda batun ya haifar da musayar ra’ayoyi a a shafukan sada zumunta.
A cewar Muoka, hukumar ta musanta zargin tare da ayyana cewa ta kai rahoton zargin ga hukumomin tsaro da suka dace domin gudanar da bincike da kuma daukar matakin da ya dace.