Masanin tattalin arziki a nan kano, Dr Abdurrazak Ibrahim Fagge ya ce yayi wuri Najeriya ta fara tunanin cire tallafin mai a wannan lokaci da kasar nan ke fama da kalubale na tattalin arzikin kasa.
Najeriya kasancewarta giwar Afrika ta bangaren tattalin arziki ta kashe naira Tiriliyan Biyu da bilyan 91 a matsayin biyan tallafin mai tsakanin watan janairu zuwa satumbar bara, wanda hakan ke nuna cewar tana kashe sama da naira bilyan 400 a kowane wata a matsayin biyan tallafin mai.
A hirarsa da Arewa Radiyo, Dr Ibrahim Fagge malami a jami’ar Yusif Maitama Sule dake an kano, Ya bukaci a rika hukunta wadanda suke yiwa tsarin bada tallafin man zagon kasa, a maimakon yin gaggawar janye tallafin man a wannan lokaci.
Bugu da kari ya ce mafi akasarin kasashen da suka cigaba na samar da tsarin bada tallafin mai ga jama’arsu domin rage radadin tsadar rayuwa da suke a ciki.